Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Shugaba Masoud Pezeshkian a yau Asabar da dare 18 Yuli, 2026, a shafin sada zumunta na X ya rubuta: Sako mai cike da hikima da haɗin kai na jagora mai girma na juyin juya halin Musulunci da goyon bayansa ga shugabannin rassa uku da jami'an ƙasar, shine kariya mafi muhimmanci ga muradun kasa da ci gaban Iran Musulunci.
Shugaban kasa ya kara da cewa: Tabbatuwa ga bin abubuwan da suka shafi hadin kai mai tsarki da guje wa sabani da rarrabuwa, shine asalin nasara a wannan lokaci mai muhimmanci.
………………….
Ra'ayinka